Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta yi tattaunawa da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifukan da suka nuna aniyar ajiye makamai da rungumar zaman lafiya, yayin da za a yi amfani da ƙarfi kan waɗanda suka ci gaba da ɗaukar hanyar tashin hankali.
Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin BlackBox tare da Rufai Oseni, inda ya ce samar da dawwamammen zaman lafiya na buƙatar ba wa masu tuba damar komawa cikin al’umma. Ya ce Najeriya na buƙatar tsarin gyarawa da sake haɗa waɗanda suka yi watsi da tashin hankali domin su bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa.
Tsohon gwamnan jihar Anambra State ya kuma jaddada cewa haɗin kan ƙasa da adalci ga kowane yanki ne ginshiƙin tsarinsa na shugabanci. Kalaman nasa sun sake tayar da muhawara kan ko tattaunawa, matakin soja ko haɗa hanyoyin biyu ne mafita mafi dacewa ga matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta.

