Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa na miƙa sunayen ‘yan takararsu na zaɓen 2027 da ƙarin kwana uku. Sabon wa’adin zai ƙare da tsakar daren ranar 14 ga Yuli, 2026.
INEC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bayan buƙatar da Majalisar Tuntuɓa ta Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar, sakamakon matsalolin da wasu jam’iyyu suka fuskanta wajen loda sunayen da bayanan ‘yan takararsu a shafin yanar gizon hukumar.
Hukumar ta ce ƙarin wa’adin zai bai wa jam’iyyun siyasa damar kammala aikin cikin sauƙi tare da bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe. Ana sa ran za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a watan Janairun 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zai gudana a watan Fabrairun shekarar.

