Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce ƙudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta zai ƙarfafa tsarin tsaro tare da taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.
Barau ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Gidan Rediyon Najeriya (FRCN) Kaduna, inda ya ce an tsara ƙudirin ne bayan tattaunawa da Fadar Shugaban Ƙasa, Majalisar Dokoki, Rundunar ‘Yan Sanda, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki. Ya kuma ce an tanadi matakan kariya domin hana amfani da rundunar wajen siyasa ko cin zarafi.
Ya ce rundunar ‘yan sandan jihohi za ta yi aiki tare da rundunar ‘yan sandan ƙasa, yayin da jami’an da za a ɗauka daga cikin al’ummomin da za su yi aiki za su taimaka wajen yaƙi da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane. Barau ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su mara wa ƙudirin baya domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.

