Hukumomin Saudi Arabia sun tabbatar da harin jirage marasa matuƙa kan matatun mai, inda aka samu tashin wuta. Sun ce an yi nasarar kakkaɓo jiragen tare da daƙile gobarar da ta tashi.
Ma’aikatar makamashi ta ƙasar ta bayyana cewa an kashe wutar a matatar mai ta Ras Tanura, wadda kamfanin Saudi Aramco ke gudanarwa. Sanarwar ta ce matatar ta samu ƙaramar illa sakamakon ɓaraguzan jiragen da aka kakkaɓo.
Jami’an kashe gobara sun samu nasarar gaggauta shawo kan wutar, yayin da wani bidiyo da BBC ta tantance ya nuna hayaƙi na turnuƙewa a saman matatar. Saudiyya ta daɗe tana bai wa dakarun Amurka da na ƙasashen Yamma mafaka, kuma ta fitar da sanarwar Allah wadai kan hare-haren Iran.

