Wasu da ake zargin ‘yan ƙungiyar Lakurawa ne sun kai hari da safiyar Alhamis kan shingen binciken ‘yan sanda da ke Bakinruwa/Maje a ƙaramar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda biyu da ke bakin aiki.
Shaidu sun shaida cewa maharan sun zo da yawa, suka yi galaba kan ‘yan sandan sannan suka kona tantin da ake amfani da shi a matsayin wajen aikin jami’an. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da sassafe lokacin da jami’an ke gudanar da aikinsu na yau da kullum.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da harin, yana mai cewa jami’ai biyu sun rasa rayukansu yayin da aka kona shingen binciken. Rahotanni sun ce wannan shi ne hari na uku a yankin kan iyakar Bakinruwa–Maje cikin ‘yan watannin nan, inda a baya ma aka kashe jami’an Nigeria Customs Service da Nigeria Immigration Service.

