Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Gwamnatin Kano Ta Shiryawa Ƴan Jaridar Yanar Gizo Horo Na Yini Biyu a Jigawa

      January 15, 2026

      Tanka Ta Murƙushe Mutane 5 a Gombe

      January 12, 2026

      Babu Siyasa a Binciken Da Ake Yi Wa Malami – EFCC

      January 12, 2026

      Ƴan Bindiga Sun Kashe Soja Da Jam’in NSCDC a Benue

      January 12, 2026

      Manyan Jiga-jigan APC 3 a Kogi Sun Mutu

      January 12, 2026
    • Siyasa

      Manyan Jiga-jigan APC 3 a Kogi Sun Mutu

      January 12, 2026

      Ganduje Zai Gana Da Masu Ruwa-da-tsaki Na APC

      January 11, 2026

      Datti Baba-Ahmed Ya Musanta Batun Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa

      January 9, 2026

      Fubara Barazana Ne Ga Demokaraɗiyya – Kakakin Majalisar Rivers

      January 9, 2026

      Kotu Ta Ƙi Bayar da Belin Kwamishinan Kuɗi Na Bauchi

      January 6, 2026
    • Addini

      Kano: Hisbah Ta Karɓi Ƙorafe-Ƙorafe Sama da 12,000 a 2025

      January 2, 2026

      Da Ɗumi-ɗumi : Sheikh Dahiru Bauchi Ya rasu

      November 27, 2025

      Zakaran Gwajin Dafi : Hajji 2025 Karkashin Farfesa Saleh Pakistan  

      November 24, 2025

      Hajji Da Shugabanci Nagari Ƙarƙashin Jagorancin Farfesa Pakistan

      November 17, 2025

      Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Rage Kudin Aikin Hajjin 2026

      November 10, 2025
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021

      Popular New Xbox Game Pass Game Being Review Bombed With “0s”

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » Zakaran Gwajin Dafi : Hajji 2025 Karkashin Farfesa Saleh Pakistan  
    Addini

    Zakaran Gwajin Dafi : Hajji 2025 Karkashin Farfesa Saleh Pakistan  

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanNovember 24, 2025No Comments3 Mins Read

    Gabatarwa

    A kowace shekara, aikin Alhaji yana ɗaukar dubban ‘yan Nijeriya zuwa ƙasar Saudiyya don aiwatar da ɗaya daga cikin ginshiƙan Musulunci. Wannan babban aiki yana buƙatar tsari, gaskiya, da ƙwarewa abubuwan da suka zama alamar shugabancin Shugaban Hukumar Alhazai na ƙasa.

    A ƙarƙashin jagorancinsa, hukumar ta samu sauye-sauye masu muhimmanci da suka inganta tsarin tafiya, masauki, abinci, da kula da lafiya ga maniyyata. Wannan ya tabbatar da cewa aikin Alhaji ya zama abin alfahari ga Nijeriya da dukkan Musulmai.

    Gyare-gyare da Sauye-Sauye Masu Tasiri

    Tun bayan hawansa kujerar shugabanci, ya aiwatar da gyare-gyare na zahiri da na tsarin aiki da suka kawo sauƙi ga maniyyata.Daga cikin wannan tsare-tsaren akwai:

    An Kara Tsabtace Tsarin Rijista, Domin Gujewa Cin Hanci da Almundahana

    An samar da horar da maniyyata kafin tafiya, don su fahimci dokokin ibada da tsarin zamantakewa,

    An inganta huldar hukumar da hukumomin Saudiyya, domin tabbatar da aminci da jin daɗin maniyyata.

    Wadannan matakai sun nuna cewa wannan shugaba ba kawai mai kula da ofis ba ne, mai hangen nesa ne wanda ke son ganin aikin Alhaji yana gudana daidai da ƙa’idar Musulunci da mutuncin Najeriya.

    Walwalar Maniyyata na Gaba Da Komai

    Babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne walwalar maniyyata. A lokutan da wasu ke ganin wannan aiki a matsayin tafiyar ofis, shi yana ganinsa a matsayin ibada da amana. An samu sababbin tsare-tsare da suka tabbatar da cewa maniyyata suna samun:

    Masauki mai kyau da tsabta

    Kula da lafiya ta zamani

    Abinci mai inganci

    Sufuri mai aminci.

    A lokuta da dama shugaban hukumar alhazai da kansa yake zagayawa cikin sansanonin maniyyata yana dubawa kai tsaye don ganin duk wani umarni da ka bayar a rubuce ana aiwatar da shi a aikace wanda wannan alama ce ta an yi dacen shugaba mai kula da al’umma da zuciya ɗaya kuma jajirtacce.

    Jagoranci Da Addini

    A matsayinsa na malami kuma masani a fannin addini, yana jagoranci bisa tsoron Allah. Wannan halin nasa ne ya jawo masa girmamawa daga malamai da shugabannin addini daga sassa daban-daban na ƙasar.

    Ayyukansa sun tabbatar da cewa ibada da shugabanci suna iya tafiya tare, idan aka yi su da gaskiya, tsoron Allah, da hangen nesa.

    Tasirin Ayyukansa a Siyasa da Al’umma

    Baya ga aikin hajji, wannan shugaba ya zama murya ta gaskiya a cikin al’umma. Yana kira ga zaman lafiya, haɗin kai, da goyon bayan manufofin gwamnati masu amfani ga jama’a. A siyasance ya kare muradun gwamnati da ke nuni da kishin kasa son al’umma da tausaya musu , inganta tattalin arziki da kiwon lafiya da hada kawunan al’umma na kowacce nahiya da kabila a Nijeriya.

    Magoya bayansa sun ɗauke shi a matsayin malami mai kishin ƙasa, wanda ke amfani da matsayinsa wajen haɗa kai, ba rarrabuwar kai ba, don ya tafi da dukkan baggarori na dariku.

    Kammalawa

    Shugaban hukumar alhazai ya zama abin koyi ga shugabanni da dama mutum mai hangen nesa, mai gaskiya, mai amana, kuma mai kishin al’umma. “Duk wanda ya yi aiki da gaskiya, Allah zai tabbatar da darajarsa a duniya da lahira.

    Pakistan
    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleƳanbindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 8 a Kebbi
    Next Article Zargin Biyan kudin Fansa : Gwamnatin Kaduna Ta Buƙaci El-Rufai Ya Janye Kalamansa Ko Ta Makashi a Gaban Kotu
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Gwamnatin Kano Ta Shiryawa Ƴan Jaridar Yanar Gizo Horo Na Yini Biyu a Jigawa

    January 15, 2026
    Featured

    Tanka Ta Murƙushe Mutane 5 a Gombe

    January 12, 2026
    Featured

    Babu Siyasa a Binciken Da Ake Yi Wa Malami – EFCC

    January 12, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202542 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202532 Views

    An Gano Motar Ofishin Mataimakin Gwamna Da Aka Sace

    November 12, 202527 Views

    NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Wani Kororon Roba Me Matuƙar Haɗari Ga Lafiya

    December 30, 202525 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.