Abubakar Atiku Abubakar (Abba), ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027. An sanar da sauya sheƙar ne a ranar Alhamis a Majalisar Ƙasa, Abuja.
Abba ya ce ya yi murabus daga PDP tare da umartar dukkan mambobin tsarinsa na siyasa, wato Haske Atiku Organisation da ya kafa a 2022, su koma APC su kuma yi aiki domin manufofin Renewed Hope Agenda na Tinubu. Ya bayyana matakin a matsayin na tarihi kuma na kashin kai, yana mai cewa zai yi aiki tare da Sanata Barau Jibrin domin nasarar Tinubu a wa’adi na biyu.
Shugabannin APC na yankin Arewa maso Gabas, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kasa (Arewa maso Gabas) Mustapha Salihu, sun tarbi Abba tare da yaba wa matakin. A wajen taron, an kuma sauya sunan ƙungiyarsa zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken sauya akala da goyon bayan Tinubu a 2027.

