Gwamnatin Tarayya ta ayyana kawo ƙarshen cin hanci da rashin ɗa’a a manyan makarantun ƙasar nan, tana mai jaddada cewa za a tsaurara matakan gaskiya, riƙon amana da shugabanci nagari a fannin ilimi. Ministan Ilimi, Dakta Maruf Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro na shugabannin polytechnics da kwalejojin ilimi.
Ministan ya ce gwamnati ba za ta ƙara lamuntar almubazzaranci, cin zarafin ofis ko munanan ɗabi’u ba a manyan makarantu. Ya bukaci majalisun gudanarwa da shugabannin makarantu su guji kawo rikici, su kula da dukiyar jama’a, tare da bai wa cancanta fifiko a ɗaukar ma’aikata da ɗaga mukamai.
Alausa ya kuma jaddada muhimmancin sauya fasalin ilimin polytechnic ta hanyar ƙarfafa kirkire-kirkire da ɗorewa, domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Ya sanar da shirin TETFund na musamman don sabunta makarantu da kayan zamani, tare da alkawarin ci gaba da goyon bayan gwamnati a ƙarƙashin ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Tinubu.

