Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP). An bayyana hakan ne a ranar Juma’a, lamarin da ya janyo hankalin al’umma da masu bibiyar harkokin siyasa a fadin jihar da kasa baki ɗaya.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dakin-Tofa, ne ya tabbatar da ficewar gwamnan, inda ya ce matakin ya biyo bayan tattaunawa da nazari mai zurfi da aka yi kan halin da jam’iyyar ke ciki a halin yanzu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa dalilin barinsa jam’iyyar NNPP shi ne rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar, wanda a cewarsa ke hana tafiyar da ita yadda ya kamata da kuma cimma manufofin da aka sanya a gaba.

