Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wata amarya bisa zargin kashe angonta mako guda bayan aurensu a ƙauyen Guaza da ke ƙaramar hukumar Jahun. Rundunar ta ce ana zargin matar da amfani da shinkafar ɓera wajen kashe mijin nata.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Lawal Shi’isu Adama ya fitar, ya bayyana cewa angon ya ci abincin rana a gida ne kafin ya fara jinya, inda aka gaggauta kai shi asibiti. Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa bayan isarsa, lamarin da ya tayar da zargi.
Ƴansanda sun ce wadda ake zargin ta amsa laifin saka guba a abincin mijinta, inda ta ce iyayenta sun tilasta mata auren mutumin da ba ta so. Rundunar ta ce kwamishinan ƴansandan jihar ya bayar da umarnin faɗaɗa bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

