Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce yana da yaƙinin cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da muƙarrabansa za su yi nadamar ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Kwankwaso ya bayyana cewa fitar gwamnan daga NNPP ta ba mutane da dama mamaki, yana mai cewa shi kansa yana jin lamarin kamar a mafarki. Ya ƙara da cewa wasu na ganin lamarin kamar wani tsari ne da aka shirya, duk da cewa shi bai yarda abubuwan suna faruwa yadda ake tunani ba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC a hukumance a ranar Litinin 26 ga Janairu, 2026. Wannan ya biyo bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a 23 ga Janairu, ƙasa da shekara uku bayan lashe zaɓen gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar.
Add A Comment

