Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa Jihar Kwara a ranar Asabar domin ziyartar ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama, bayan wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar mutane 75. Ziyarar ta biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya bayyana.
A cewar Nkwocha, Shugaban Ƙasa ya umurci Shettima da ya tantance halin da ake ciki da kansa tare da isar da ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga iyalan waɗanda abin ya shafa. Mataimakin shugaban ƙasar ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Gwamnan ya bayyana waɗanda aka kashe a matsayin Musulmai na yankin da aka yi wa kisan gilla saboda sun ƙi amincewa da koyarwar wasu masu tsattsauran ra’ayi. Rahotanni sun ce harin ya faru ne bayan da ‘yan bindiga suka kasa tilasta wa mazauna yankin karɓar akidarsu, lamarin da ya jawo kisan kiyashi a daren Talata.

