An fara zanga-zanga a Abuja, babban birnin tarayya, kan gyaran Dokar Zaɓe a Najeriya, yayin da jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar hula da na kwadago ke zargin Majalisar Tarayya da tauye dimokuraɗiyya. Zargin ya biyo bayan ƙin amincewa da ƙudirin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.
Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan ‘yan majalisa sun ƙi amincewa da sashen da zai tilasta tura sakamakon zaɓe daga rumfunan kaɗa ƙuri’a ta na’urar da jama’a za su iya gani. Masu sukar matakin sun ce hakan na rage gaskiya da sahihanci a zaɓuka, tare da ƙara fargabar maguɗin zaɓe.
Masu zanga-zangar sun fara taruwa a kusa da harabar Majalisar Tarayya a Abuja, yayin da ake fargabar yaɗuwar gangamin zuwa wasu jihohi. A halin da ake ciki, Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta yi gargaɗin zanga-zangar ƙasa baki ɗaya, yayin da Majalisar Dattawa ta kira zaman gaggawa a ranar Talata, 10 ga Fabrairu.

