Hukumar Alhazai ta Ƙasa, National Hajj Commission of Nigeria, ta umarci hukumomin kula da alhazai na jihohi su gaggauta mayar da kuɗaɗen waɗanda ba su samu damar yin rijistar Hajjin 2026 ba. Shugaban hukumar, Ismail Yusuf, ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja.
Ya ce an rage adadin kujerun alhazan Najeriya zuwa 40,250 ne sakamakon sabbin tsare-tsare da ƙuntatawar da hukumomin Saudi Arabia suka ƙaddamar, ba wai don an ware Najeriya ba. Ya kuma buƙaci jihohi su daidaita bayanansu tare da cire sunayen da suka wuce adadin da aka amince da shi.
Hukumar ta kuma gargaɗi cewa wa’adin bayar da biza yana da iyaka, don haka dole jihohi su kammala gwaje-gwajen lafiya da tattara bayanai cikin lokaci. NAHCON ta ce wajibi ne a mayar da kuɗin waɗanda ba za su je aikin Hajji ba domin kauce wa rikici da kuma tabbatar da gaskiya a tsarin.

