Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta taɓa goyon bayan musguna wa Kiristoci ko nuna wariyar addini ba, bayan rahoton da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar. Ta ce matsalolin tsaro da ake fuskanta sun samo asali ne daga ta’addanci, fashi da makami da rikice-rikicen al’umma.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a sanarwar ranar Talata. Ya ce kundin tsarin mulki ya tanadi ‘yancin addini ga kowa, kuma gwamnati na ci gaba da kare waɗannan haƙƙoƙi tare da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro da yaƙi da masu aikata laifi.
Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, tana mai maraba da haɗin kai. Wannan na zuwa ne bayan an miƙa rahoton bincike ga shugaban Amurka, Donald Trump, kan zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya.

