An samu babban sauƙi a Jihar Kebbi bayan da aka tabbatar da kubutar dalibai mata 24 da aka sace daga Government Girls Secondary School Maga a Karamar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren baya, inda aka tashi da fargaba a yankin, kafin gwamnatin tarayya a ranar Talata 25 ga Nuwamba 2025 ta tabbatar da ceto su ba tare da samun rahoton mutuwa ba. Bayo Onanuga, Mai Ba wa Shugaban Kasa Shawara kan Bayanai da Tsare-Tsare, shi ne ya sanar da hakan cikin wata takardar da ya fitar ga manema labarai.
Jami’an tsaro sun gudanar da aikin hadin gwiwa wajen ganin daliban sun dawo cikin koshin lafiya, sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai game da yadda aka ceto su ba, ko an kama masu garkuwar. Kakaki24 ta tattaro cewa iyaye da al’ummar yankin na jiran karin haske daga hukumomi, kasancewar yankin na daga cikin wuraren da hare-haren ’yan bindiga ke ta karuwa a ’yan shekarun nan, abin da ke ci gaba da barazana ga karatun ’ya’ya mata da tsaron makarantu.
Al’ummar yankin sun nuna farin ciki tare da godiya bisa kubutar daliban, yayin da kungiyoyin kare haƙƙin ɗalibai ke kira ga gwamnati ta kara tabbatar da tsaro a makarantun Arewa maso Yamma don kauce wa maimaituwar irin wannan lamari. A halin yanzu, ana sa ran gwamnatin tarayya da ta jiha za su fitar da cikakken bayani nan gaba, musamman dangane da matakan da za a dauka wajen inganta tsaro da kare ilimi a yankunan karkara.

