Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar rundunar ‘yan sandan Najeriya da take neman a hana gudanar da zanga-zangar neman sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Rundunar ‘yan sandan ƙarƙashin jagorancin IGP Kayode Egbetokun ce ta shigar da buƙatar kotun domin dakatar da gangamin da aka shirya.
Rahotanni sun nuna cewa ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasa, Omoyele Sowore, ne ya shirya kuma zai jagoranci zanga-zangar a ranar 20 ga Oktoba, wadda za ta gudana a kusa da fadar shugaban ƙasa domin neman a saki Kanu, wanda ke tsare tun shekarar 2021.
Kotun ta bayyana cewa ba za ta yanke hukunci kan buƙatar ‘yan sanda ba sai ta ji daga bangaren Sowore. Don haka ta umurci a miƙa masa takardar ƙarar sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga Oktoba domin cigaba da zama.
Sowore ya jaddada cewa za su gudanar da zanga-zangar cikin lumana domin nuna rashin jin daɗinsu ga ci gaba da tsare Nnamdi Kanu ba tare da cikakken hukunci ba, yana mai cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta mutunta ‘yancin jama’a na bayyana ra’ayinsu.

