Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya bayyana cewa gwamnati na gudanar da bincike kan dalilin da ya janyo dawowar hare-haren satar ɗalibai a makarantu da ’yan bindiga suka sake farawa a wasu yankuna na ƙasar. Ya ce duk da cewa akwai raguwar matsalolin tsaro, irin wannan yaki da ’yan ta’adda ba ya ƙarewa cikin sauƙi, domin sukan ɓullo da sababbin dabaru lokaci zuwa lokaci. Badaru ya bayyana cewa akwai wuraren da gwamnati ta sani, amma ba za a iya kai farmaki ba saboda kasancewar su a cikin yankunan da ke cike da jama’a ko kuma daji da ba za a iya harba bam ba.
A cewarsa, sojojin ƙasar na aiki ba dare ba rana domin murkushe waɗanda ke haddasa wannan sabon tashin hankali. Ministan ya ce gwamnati ba ta taɓa bayyana cewa an kammala kawar da matsalar tsaro gaba ɗaya ba, amma abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne dawowar harin da ya ƙaddamar da satar ɗalibai daga makarantunsu. Ya ce ana gudanar da zurfin nazari domin gano ainihin musabbabin komawar wannan barazana da kuma matakan da za a ɗauka don dakile ta gaba ɗaya.
Badaru ya yi karin bayani kan tsaron makarantu, yana mai cewa gwamnati na da tsari na musamman na kare cibiyoyin ilimi daga hare-haren ’yan bindiga. Ya ce wannan tsari ne ya sa aka samu sauƙi cikin shekaru biyun da suka gabata, inda ba a sami manyan hare-hare da suka shafi ɗalibai ba. Sai dai ministan ya ce ana sake duba tsarin ne domin tabbatar da cewa kura ta kama ne kawai, ba wai barazana ta dawo da ƙarfi ba.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta karfafa matakai tare da inganta dabarun yaki da ‘yan ta’adda, musamman a yankunan da suka sha fama da matsalar satar ɗalibai. Masu nazari kan tsaro na bayyana cewa dawowar irin wadannan hare-hare na iya shafar burin gwamnati na dawo da kwarin gwiwar iyaye da ɗalibai kan komawa makarantu. Ana sa ran gwamnati za ta sanar da sabbin matakan tsaro cikin makonni masu zuwa domin tabbatar da cewa makarantu sun kasance wurare masu aminci ga yara a fadin Najeriya.

