Al’ummar Zamfara sun bayyana cewa ƴan bindiga sun kai hari cikin dare, inda suka sace fiye da mutum kusan 150 a ƙauyukan Kurfa Ɗanya da Kurfan Magaji a yankin Bukkuyum. Wannan lamari ya tilasta wa ɗaruruwan mutane yin gudun hijira daga gidajensu.

Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ɗan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Gumi da Bukkuyum, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mazauna garuruwan sun kwana cikin tashin hankali kuma yanzu sun tsere zuwa garin Bukuyyum.

Ya ƙara da cewa yankunan Bukkuyum, Gumi da Anka sun jima suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa. Hon. Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da hankali kan matsalar tsaro a Zamfara, yana mai cewa da yawa suna ganin gwamnati ta fi mai da hankali a Borno kan barazanar dawowar Boko Haram, amma Zamfara na bukatar kulawa ta musamman.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version