’Yan bindiga da suka sace masu ibada a wani cocin ECWA da ke Omugo a karamar hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara sun bukaci a biya su Naira biliyan 1 domin sakin mutanen takwas da har yanzu suke hannunsu. Faston cocin, Toba Omole, ya bayyana cewa har da matarsa a cikin wadanda aka sace, inda ya ce sun samu damar jin muryoyinsu bayan masu garkuwar sun tuntubi al’umma.
Faston ya ce bukatar kudin fansar ta wuce karfin iyalan wadanda aka sace da ma al’ummar yankin, don haka ya roki gwamnati da masu hannu da shuni su kawo dauki domin ceto su. Ya kara da cewa harin da aka kai lokacin ibada a ranar Lahadi ya jefa al’umma cikin firgici, inda mutane da dama suka fara tserewa daga gidajensu saboda fargabar sake kai hari.
A wani sabon hari kuma, ana zargin ’yan bindiga sun kai farmaki garin Oro-Ago da ke makwabtaka da Omugo, inda suka kashe wani shugaban ’yan sintiri tare da raunata wani jami’in tsaro. Rahotanni sun nuna cewa wannan lamarin ya kara dagula tsaro a yankin.
