Rundunar ‘yan sanda a Jihar Lagos ta kama wani mutum mai shekara 30 da ake zargi da sayar da jaririn ‘yar uwarsa kan kudi Naira miliyan biyu. Rahoton News Agency of Nigeria ya ce wanda ake zargin, mazaunin Igbogbo a yankin Ikorodu, ya ce ya aikata hakan ne domin tara kudin binne mahaifiyarsu.
An ce mahaifiyar jaririn ce ta kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga kama wanda ake zargin. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Olohundare Jimoh, ya umarci a mika shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike.
Wanda ake zargin ya amsa laifin, yana mai cewa ya hadu da wadda ta sayi jaririn ne a Facebook, inda aka bukaci ya kawo yaron zuwa Mile 2 kafin a tura masa kudin Naira miliyan biyu a asusunsa. Ya ce ya bai wa ‘yar uwarsa Naira 500,000 daga cikin kudin, amma daga baya ta nemi a dawo mata da jaririn tare da kai kara ga ‘yan sanda, abin da ya kai ga cafke shi.


