Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta kai samame wata maboyar masu garkuwa da mutane a ƙauyen Gidan Akuya da ke Ƙaramar Hukumar Keana, inda ta kama wani da ake zargi tare da kwato makamai.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel, ya ce an kama wanda ake zargin mai suna Jibril Yunusa mai shekaru 43 bayan jami’an tsaro sun samu sahihan bayanan sirri. Ya ce wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin tserewa da ya ga jami’an tsaro, amma suka bi sawunsa suka kama shi.

‘Yan sanda sun ce sun kwato bindiga kirar AK-47 guda ɗaya, mujallar harsashi mara komai da kuma wata bindiga ƙirar gida daga maboyar. A cewar rundunar, wanda ake zargin ya amsa laifin shiga hare-haren garkuwa da mutane a yankunan Keana da Awe, yayin da Kwamishinan ‘yan sandan jihar Shetima Jauro Mohammed ya umarci jami’ai su ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version