Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, na jinkirta komawarsa jam’iyyar ADC ne sakamakon rashin tabbacin cewa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027. Sunday PUNCH ta ruwaito cewa Kwankwaso ya shiga tattaunawa da shugabannin ADC, amma har yanzu ba a samu wata matsaya ta ƙarshe ba.
Rahoton ya ce akwai shirin haɗin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso domin tsayawa takara a 2027 karkashin ADC, shiri da ake alakanta shi da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo. Duk da haka, majiyoyi sun ce wasu manyan ’yan Arewa da Obasanjo sun shawarci Kwankwaso kada ya yi gaggawar sauya sheƙa har sai an tabbatar Obi ne zai samu tikitin jam’iyyar.
Wani jigo a bangaren Kwankwaso ya bayyana cewa ana fargabar Obi zai shiga zaɓen fidda gwani a ADC ne daga bisani ya sha kaye, sannan a tursasa masa karɓar mataimakin shugaban ƙasa. Ya ce har yanzu ana ci gaba da shawarwari, kuma Kwankwaso na cigaba da shawarwari kafin yanke hukunci na ƙarshe.

