Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da sanarwar tsaro inda ya gargaɗi ‘yan kasarsa kan yiwuwar harin ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyinsa da makarantu masu alaƙa da Amurka a faɗin ƙasar.
A sanarwar da ofishin jakadancin da ke Abuja ya fitar, an buƙaci ‘yan Amurka su ƙara yin taka-tsantsan idan za su ziyarci ofisoshin diflomasiyyar ƙasar. Sanarwar ta kuma ambaci ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma ƙaramin ofishinta da ke Lagos.
Ofishin jakadancin ya shawarci ‘yan kasarsa su rika canza hanyoyin tafiya da lokutan fita, su guji cunkoson jama’a ko zanga-zanga, sannan su tabbatar da cewa wayoyinsu suna da caji tare da sanin hanyoyin fita na gaggawa idan wani lamari ya taso.
