Mazauna Maiduguri sun shiga fargaba a yammacin Litinin bayan jin ƙarar fashewar abubuwa da dama a sassan birnin. Rahotanni sun nuna cewa ana zargin mayaƙan Boko Haram da dasa bama-bamai na na’urar fashewa ta IED a wasu wurare.
Wuraren da abin ya shafa sun haɗa da ƙofar University of Maiduguri Teaching Hospital, zagayen Monday Market Roundabout da kuma yankin Elkanemi. Rahotanni sun ce fashewar farko ta auku ne kusan ƙarfe bakwai na yamma, jim kaɗan bayan musulmi sun buɗe baki.
Sai dai har zuwa yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka jikkata ko suka rasa rayukansu ba. Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan da ‘yan ta’adda suka kai hari wani sansanin soji a Ajilari da ke wajen birnin, inda sojoji suka ce sun fatattaki maharan tare da kashe wasu daga cikinsu.


