Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga matakin da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta ɗauka kan jam’iyyar ADC, bayan soke shugabancin tsagin David Mark tare da cire sunayen shugabanninta daga rajista. Matakin na INEC ya biyo bayan wani hukuncin kotu da ya shafi rikicin cikin gida na jam’iyyar.

Daraktan yaɗa labarai na sakatariyar APC, Mallam Bala Ibrahim, ya bayyana cewa INEC tana aiki ne kamar alƙali mai zaman kansa, inda aikinta shi ne tabbatar da adalci ba tare da goyon bayan wani ɓangare ba. Ya ce matakin da aka ɗauka ya dace da dokar da ke tafiyar da harkokin zaɓe.

Dangane da zargin da ADC ke yi wa APC na amfani da INEC domin cutar da ita, Bala Ibrahim ya musanta hakan, yana mai cewa rikicin cikin gida ne kuma yana gaban kotu. Ya jaddada cewa ya kamata a bari kotu ta yanke hukunci, yana mai cewa matakin INEC ya yi daidai da bin umarnin kotu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version