Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    • Shafin Farko
    • Labarai

      Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Man Fetur

      March 3, 2026

      Doguwa Ya Yi Murabus Daga Muƙamin Kwamishinan Ruwa Na Kano

      March 3, 2026

      Amurka Na Da Isassun Makaman Yaƙi Da Za a Iya Amfani Da Su “Har Abada” – Trump 

      March 3, 2026

      ICPC Ta Bayyana Abubuwan Da Ta Samo Daga Gidan El-Rufai a Abuja

      March 3, 2026

      Ɗan Atiku Ya Ajiye Muƙamin Kwamishina a Gwamnatin Adamawa

      March 3, 2026
    • Siyasa

      Doguwa Ya Yi Murabus Daga Muƙamin Kwamishinan Ruwa Na Kano

      March 3, 2026

      Gwamnan Adamawa Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

      February 27, 2026

      NDLEA Ta Kama Wata Mata Mai Cikin Bogi Ɗauke da Hodar Iblis a Iyakar Seme

      February 22, 2026

      Jam’iyyun Adawa Sun Kaurace wa Zaɓen Kano, APC Ta Lashe Kujerun Majalisa a Rivers

      February 22, 2026

      Kotu Ta Umarci INEC Ta Yi Wa Jam’iyyar NDP Rajista

      February 19, 2026
    • Addini

      Bauchi Ta neman ƙarin Kujerun Hajji Daga Saudiyya

      February 16, 2026

      Sarkin Musulmi Ya Umarci Ƴan Najeriya Su Fara Duban Jinjirin Watan Ramadan Ranar Talata

      February 16, 2026

      Tinubu Ya Naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a Matsayin Sabon Shugaban NAHCON

      February 11, 2026

      Sheikh Usman Kusfa Zaria (Rigi-rigi) Ya Rasu

      February 2, 2026

      Jigawa Ta Fara Gwajin Lafiya ga Maniyyatan Hajjin 2026

      January 28, 2026
    • Nishadi

      Oculus Founder Makes a VR Headset That Can Literally Kill You

      January 13, 2021
      85

      Braun Series 7 Electric Shaver Review: Quality at a Good Price

      January 13, 2021
      85

      Google Pixel 7, iPhone 14 Compared: Check Out 5 Major Differences

      January 13, 2021

      Why Apple Should Skip The MacBook Pro Launch

      January 12, 2021

      Apollo G2J Showcases Electric Sports Car

      January 12, 2021
    • Tsaro

      Ba a Fasa Bututun Mai Ko Ɗaya a Niger Delta a 2025 Ba – Sojoj

      January 20, 2026

      Sojojin Najeriya Sun Ƙwato lita 290,000 Na Man Fetur a Yankin Neja Delta

      October 21, 2025

      Ƴan Bindiga Sun Ƙwace Wayoyin Ƴan Sanda a Zamfara

      October 2, 2025

      Gwamnan Kano Ya Buƙaci Tinubu Ya Tsige Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar

      October 1, 2025

      Will Using a VPN on Phone Helps Protect You from Ransomware?

      January 14, 2021
    BECHI HAUSA NEWSBECHI HAUSA NEWS
    Home » ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Gargaɗi Na Makonni Biyu
    Featured

    ASUU Ta Tsunduma Yajin Aikin Gargaɗi Na Makonni Biyu

    Abbass AbdurrahmanBy Abbass AbdurrahmanOctober 12, 2025No Comments2 Mins Read

    Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkan jami’o’in gwamnati a Najeriya. Shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a jami’ar Abuja ranar Lahadi 12 ga Oktoba. Wannan mataki ya biyo bayan ƙarewar wa’adin gargadin kwanaki 14 da kungiyar ta bayar tun ranar 28 ga Satumba, 2025.

    ASUU ta umarci dukkan rassanta a fadin ƙasar da su daina aiki daga tsakar daren Litinin, 13 ga Oktoba, 2025. Farfesa Piwuna ya bayyana cewa yajin aikin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince a taronta na baya-bayan nan. Wannan na nuna sabon takaddama tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya duk da tattaunawar sulhu da ake yi domin kauce wa sake shiga rikicin ilimi.

    A cewar Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin kammala tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolin da suka dade suna jawo rikici. Ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta saki Naira biliyan 50 domin biyan hakkokin EAA ga malamai, sannan an ware karin biliyan 150 a kasafin kuɗin 2025 don gyaran jami’o’i, wanda za a rarraba a matakai uku.

    Sai dai duk da wannan ci gaban, ASUU ta dage cewa babu wani mataki tabbatacce da zai iya dakatar da su daga aiwatar da shawarar yajin aiki. Wannan sabon yajin aikin na iya jefa harkar ilimi cikin wani sabon cikas, yayin da ɗalibai da iyaye ke fargabar tasirin da hakan zai haifar a tsarin karatun jami’o’in gwamnati.

    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Previous ArticleMatasa Sun Gaji Da Mulkin Kama-karya a Najeriya- Atiku
    Next Article Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Laifin Yin Aure Ba Tare Da Amincewar Iyayensu Ba
    Abbass Abdurrahman
    • Website

    Related Posts

    Featured

    Matatar Dangote Ta Ƙara Farashin Man Fetur

    March 3, 2026
    Featured

    Doguwa Ya Yi Murabus Daga Muƙamin Kwamishinan Ruwa Na Kano

    March 3, 2026
    Featured

    Amurka Na Da Isassun Makaman Yaƙi Da Za a Iya Amfani Da Su “Har Abada” – Trump 

    March 3, 2026
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    SABBIN LABARAI

    Gwamnatin Kano Ta Dakatar da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi

    October 1, 202544 Views

    Kotu Ta Yankewa Tsohon Firayim Ministan Mali Hukuncin Zaman Gidan Yari Sakamakon Rubutu a Shafin Sada Zumunta

    October 27, 202541 Views

    Dantawaye Ya Zama Sabon Kwamishinan Ƴansanda a Abuja

    October 17, 202532 Views

    NAFDAC Ta Yi Gargaɗi Kan Wani Kororon Roba Me Matuƙar Haɗari Ga Lafiya

    December 30, 202527 Views

    An Gano Motar Ofishin Mataimakin Gwamna Da Aka Sace

    November 12, 202527 Views
    Stay In Touch
    • Facebook
    • TikTok
    • WhatsApp
    • Twitter
    • Instagram
    • Telegram
    © 2026 Bechi Hausa News. Developed by: ENGRMKS & CO.
    • Shafin Farko
    • Game da Mu
    • Ƙarin Bayani
    • Manufar Sirri
    • Ka’idoji da Sharudda
    • Tuntuɓe Mu

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.