Yayin da ake samun rahotannin sauya sheƙar wasu gwamnoni zuwa APC, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya ce yana nan daram a jam’iyyarsa ta PDP.
Hakan na zuwa ne bayan yaɗuwar jita-jitar cewa yana shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Gwamnan ya musanta batun ta bakin shugaban PDP na jihar Bauchi a wata hira da BBC ta yi da shi.
Ya ce babu wata shawara ko tattaunawa da aka yi kan sauya sheƙa.
Pharmacist Sama’ila Adamu Burga ya bayyana zancen a matsayin jita-jita da soki burutsu.
Ya ce babu wanda gwamnan ya tattauna da shi kan sauya jam’iyya, yana mai jaddada cewa batun ba shi da tushe.
Add A Comment

