Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fara biyan albashin watan Maris na shekarar 2026 ga ma’aikatan gwamnati tun da wuri domin ba su damar yin shirye-shiryen bukukuwan Sallah cikin sauƙi. Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar ya fitar.

Sanarwar ta ce Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Bilkisu Shehu Maimota, ta bayyana cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayar da umarnin sakin kuɗaɗen domin a biya dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba.

Ta ƙara da cewa matakin na nufin sauƙaƙa wa ma’aikata gudanar da shirye-shiryen Sallah da kuma nuna yadda gwamnatin jihar ke bai wa jin daɗin ma’aikata muhimmanci, tare da buƙatar su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin cigaban jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version