Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi, daga ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025.

Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan ma’aikatar noma da kiwo, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewar sanarwar, wannan mataki na daga cikin shirin tabbatar da zaman lafiya musamman a kakar bana, yayin da manoma ke ci gaba da girbe amfanin gonakinsu.

Ƙa’idojin da dokar ta kunsa sun haɗa da:

Hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi.

Hana safarar amfanin gona a lokutan da aka ƙayyade.

Gwamnatin ta kuma umarci shugabannin kananan hukumomi da su tabbatar da rufe hanyoyin shiga yankunansu. Haka kuma, an umarci masu rike da sarautun gargajiya da su jagoranci aiwatar da wannan doka domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version