Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da fitaccen malamin addini, Sheikh Lawan Shuaibu Triumph, daga ci gaba da gudanar da wa’azi a jihar har sai an kammala binciken da ake yi kan kalaman da ake zarginsa da furtawa.
Sakataren Majalisar Shura da gwamnatin ta kafa, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.
A cewarsa, an dauki matakin ne domin ba wa malamin damar kare kansa gaban kwamitin bincike da aka kafa.
“Zarge-zargen da ake yi masa sun shafi yin kalaman da ake cewa na iya zama ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW). Saboda haka majalisar ta ga dacewar a dakatar da shi har sai an kammala bincike,” in ji Sagagi.
Ya kuma yi gargadin cewa ‘yan siyasa su nisanci tsoma baki cikin batun, yana mai jaddada cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya da adalci ba tare da nuna son rai ko bambanci ba.


