Gwamnatin Jihar Kano ta haramta raba, ware ko sauya fasalin filayen makarantu, asibitoci da sauran kadarorin gwamnati a faɗin jihar, tare da mayar da ikon kula da su karkashin Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Birane.
Kwamishinan Ƙasa da Tsare-tsaren Birane, Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana hakan yayin ziyarar duba makarantar Government Girls Secondary School Goron Dutse, Kano, bayan rahotannin mamaye filayen makarantar da wasu mutane suka yi.
Kwamishinan ya ce binciken farko ya nuna an raba kusan filaye 100 a cikin harabar makarantar domin mayar da su gidajen zama. Ya ce gwamnati ba za ta amince da kwace kadarorin jama’a da aka tanada domin ilimi ba, kuma masu karya umarnin gwamnati za su fuskanci hukunci.
Ya bayyana cewa daga ranar 3 ga Agustan 2026, duk filayen makarantu, asibitoci da sauran cibiyoyin gwamnati sun koma karkashin ikon Ma’aikatar Ƙasa. Ya kuma bukaci mazauna ƙananan hukumomi 44 su rika kai rahoton mamaye filaye da gine-ginen ba bisa ka’ida ba ga hukumomin da abin ya shafa.
