Wani mai taimaka wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana cewa yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ya ragu sosai a ƙarƙashin gwamnatin Renewed Hope. Ya ce tun daga 2023, ASUU ta shiga yajin aiki sau ɗaya kacal, wanda ya kasance na gargadi ne na kwanaki tara.
Olusegun ya danganta hakan da tsauraran matakan da gwamnati ta ɗauka a ɓangaren ilimi, yana mai cewa hakan ya bambanta da yawan yajin aiki da ake samu a gwamnatocin baya. Ya ce an samu ci gaba ne bayan sake tattauna yarjejeniyar 2009, lamarin da ya buɗe sabon babi a dangantakar gwamnati da ASUU.
Ya kuma lissafa wasu matakai da suka haɗa da fitar da jami’o’i daga tsarin IPPIS, ƙarin kuɗaɗen gyaran jami’o’i Naira biliyan 150 a kasafin 2025, biyan Earned Academic Allowances Naira biliyan 50, da kuma yarjejeniyar albashi da aka sanya hannu a ranar 14 ga Janairu, 2026, yana mai cewa dukkan waɗannan sun taimaka wajen rage rikice-rikicen yajin aiki a jami’o’in gwamnati.

