Hukumar NAHCON ta sanar da rage kudin aikin Hajji na shekarar 2026, bayan shawarar da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya bayar domin saukaka wa masu niyyar zuwa kasa mai tsarki. A baya, farashin ya kai sama da N8.7m ga masu tafiya daga kudu da N8m ga masu tafiya daga arewa.
Sabon tsarin ya bayyana cewa alhazai daga Kudu za su biya N7,991,141.76 bayan an rage kusan N792,943, yayin da daga Arewa za su biya N7,696,769.76 bayan ragin N760,915. Haka nan yankin Borno da Adamawa, wanda shi ne mafi karanci, ya sauka zuwa N7,579,020.96 bayan rage N748,104.
NAHCON ta kuma gargadi masu niyyar tafiya da su tabbatar da biyan kudin su kafin 5 ga Disamba 2025 domin tabbatar da kujerunsu. Hukumar ta ce wannan ragin zai ba da damar karin mutane su sami damar gudanar da ibadar Hajji cikin sauki.
