Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) ta bayyana jerin takardu da na’urorin lantarki da ta ce ta kwato daga gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Asokoro a Abuja. A takardun da ta gabatar a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya, hukumar ta ce ta yi aikin ne bisa sahihin sammacin bincike da aka bayar a ranar 18 ga Fabrairu, kuma aka aiwatar da shi ranar 19 ga Fabrairu.

ICPC ta ce ta kwace takardu da suka haɗa da bayanan asusun masu zuba jari, fom ɗin bayyana kadarori, takardun rajistar kamfanoni, bayanan lamuni na cikin gida da na ƙasashen waje daga 2015 zuwa 2023, da wasu rahotannin bincike na wucin gadi. Haka kuma an ce an kwato takardun hannayen jari na Ecobank Nigeria Plc, takardun filaye, rahotannin kimanta kadarori, da wasu takardun kamfanoni.

A ɓangaren na’urori, hukumar ta ce ta samo kwamfutoci da dama ciki har da Apple MacBook, wayoyin salula iri-iri, hard drives, flash drives, da sauran na’urori, waɗanda ta ce an rufe su domin gwajin binciken fasaha. Ta jaddada cewa jami’anta sun gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar rundunar ’yan sanda, kuma iyalan El-Rufai sun halarci lokacin da aka yi binciken.

Sai dai iyalan tsohon gwamnan sun musanta zargin, suna cewa an kwace tsofaffin kayayyakin sirri ne kawai. A wata sanarwa da ɗansa Bello El-Rufai ya fitar, ya kalubalanci hukumar da ta gurfanar da mahaifinsa a kotu idan tana da hujja. Tun bayan barin mulki a 2023, El-Rufai na fuskantar bincike kan zargin karkatar da kuɗi, ciki har da zargin N423bn da majalisar dokokin Kaduna ta nemi a bincika. ICPC ta nace cewa duk matakan da ta ɗauka sun dace da doka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version