Kotun birnin Bamako ta yanke wa tsohon Firayim Ministan Mali, Moussa Mara, hukuncin shekara guda a gidan yari, bayan ta same shi da laifin “lalata martabar ƙasa da ƙalubalantar hukuma,” sakamakon wani rubutu da ya wallafa a shafin sada zumunta yana goyon bayan fursunonin siyasa.
Rahotanni sun nuna cewa Mara, wanda ya shugabanci gwamnatin Mali daga shekara ta 2014 zuwa 2015, ya yi rubutun ne a watan Yuli inda ya bayyana cewa ya ziyarci wasu fursunonin siyasa tare da yin alkawarin ganin an samu adalci a gare su. Tun daga ranar 1 ga Agusta, aka tsare shi bisa waɗannan zarge-zargen kafin kotu ta tabbatar da hukuncin.
Alkalin kotun ya kuma ƙara masa hukuncin shekara guda mai dakatarwa tare da tarar CFA 500,000 (kimanin dalar Amurka 887). Lauyan sa, Mountaga Tall, ya bayyana cewa za su daukaka ƙara, yana mai cewa hukuncin ba zai dakatar da su ba. Wani abokin Mara ya ce, “Ba abin mamaki ba ne, tunda gwamnati yanzu tana danniya ga masu sukar ta.”
Mali na ƙarƙashin mulkin sojoji tun bayan juyin mulki biyu a 2020 da 2021, kuma gwamnati ta yi suna wajen tsaurara matakai ga masu adawa da gwamnati da ‘yan jarida, ciki har da rushe jam’iyyun siyasa da takaita ’yancin faɗar albarkacin baki a ƙasar.