kwamishinan Kimiyya da fasaha a gwamnatin Jihar Kano, Yusuf Kofar Mata, ya sanar da saukarsa daga muƙaminsa, yana danganta matakin da ya ɗauka da kaucewa daga tsarin siyasar da aka yi gwagwarmayar kafa gwamnatin a kai. Ya bayyana cewa murabus ɗin ya samo asali ne daga ra’ayi da ya ɗauka domin kare aƙidar da aka assasa gwamnatin da ita.

A cikin sanarwar, kwamishinan ya nuna godiyarsa ga Allah, tare da miƙa yabo ga Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf. Ya kuma gode wa al’ummar jihar bisa gudunmawar da suka ba shi a lokacin da yake hidimtawa Kano.

Kwamishinan ya ce ya yi aiki ne a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire, inda ya ce ya bayar da gudunmawa a wasu muhimman ayyuka. Ya kammala sanarwar da bayyana godiya da cewa ya yi aikinsa ne da niyyar hidimtawa al’ummar jihar Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version