Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin Bagwai, Bebeji da Rogo daga bakin aiki na tsawon watanni uku. Jami’in Yaɗa Labaran Majalisar, Malam Kamaluddeen Sani Shawai, ya tabbatar da hakan.

Ya ce matakin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin da majalisar ta kafa domin binciken ƙorafe-ƙorafen da ƙungiyoyi da al’ummomin ƙananan hukumomin suka shigar kan shugabanninsu.

A cewar jami’in, ƙorafe-ƙorafen sun shafi zargin badaƙalolin almundahana da kuɗaɗen al’umma. Ya ce majalisar ta ɗauki matakin ne bayan samun rahoton kwamitin da aka kafa domin binciken lamarin.

Shugabannin da aka dakatar sun haɗa da Alhaji Bello Abdullahi Gadanya na Bagwai, Dr. Alhassan Salisu na Bebeji da Alhaji Abubakar Mustapha Rogo na Rogo, domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version