Ƙungiyar Manchester United ta kori mai horas da ƴan wasanta, Ruben Amorim, bayan ƙungiyar ta yi samu naƙasu a gasar Premier. Amorim ya fara aiki a watan Nuwamban 2024, inda ya jagoranci ƙungiyar zuwa wasan ƙarshe na kofin Europa da Bilbao a watan Mayu.
Duk da Manchester United na zama a mataki na shida a teburin Premier, hukumomin ƙungiyar sun yi shawarar kawo sauyi yanzu. A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa matakin zai ba da damar kammala kakar a mataki mafi dacewa.
Ƙungiyar ta gode wa Amorim bisa gudumawarsa sannan ta yi masa fatan alheri a gaba. Darren Fletcher ne zai riƙe ragamar ƙungiyar a matakin riƙo a wasan da za su buga da Burnley a ranar Laraba.
