Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa na zagayowar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta kawo sun fara dora kasar akan kyakkyawan tsari.

Ga wasu manyan muhimman abubuwa 10 da shugaban ya bayyana yayin jawabinsa a wannan rana ta 01 ga Oktoba, 2025. :

Tattalin Arziƙi – GDP na Najeriya ya ƙaru da kashi 4.23% a zango na biyu na 2025, yayin da hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa lashi 20.12%, mafi ƙasa cikin shekaru uku.

Kudin da Ya Ke Ajiye a Asusun Gwamnati – An ce baitulmalin ƙasa ya kai dala biliyan 42.03, mafi girma tun 2019, abin da ya nuna karuwar amincewar masu zuba jari a kasar.

Kudaden Gwamnati – An rage yawan kuɗin biyan bashi daga kaso 97% zuwa ƙasa da kaso 50%, tare da soke tallafin man fetur.

Ƙaruwar Fitar Da Man Fetur – Ana fitar da ganga miliyan 1.68 a rana, tare da fara tace man fetur a cikin gida bayan shekaru 40.

Aikin Gine-gine – Manyan ayyuka kamar hanyar Lagos–Calabar da jirgin ƙasa Kano–Maradi na ci gaba da tafiya.

Tallafin da Aka Bawa Jama’a – Fiye da gidaje miliyan 8 sun amfana da shirin tallafin kuɗi da ya kai sama da Naira biliyan 330.

Bashin Karatu – Dalibai sama da dubu 510 sun amfana da lamunin karatu na NELFUND, domin sauƙaƙa shiga jami’a da kwalejoji.

Tsaro – Sojoji sun fara dawo da yankuna daga hannun ‘yan ta’adda da masu tada ƙayar baya, tare da dawo da ‘yan gudun hijira gidajensu.

Matasa – Gwamnati na tallafawa matasa ta fannoni irin su fasaha, kirkira, kiɗa da wasanni.

Ƙasa Ɗaya – Tinubu ya yi kira da a ƙara kishin ƙasa da biyan haraji domin gina ƙasa mai ƙarfi.

A ƙarshe, Shugaban Ƙasa ya jaddada cewa burin gwamnatinsa shi ne ganin Najeriya ta fita daga kuncin da ta tsinci kanta, ta zama ƙasa mai bunƙasa, inda kowa zai amfana da albarkatun ƙasa cikin zaman lafiya da haɗin kai.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version