Matatar man fetur ta Dangote Petrochemical Refinery ta ƙara farashin fetur na Premium Motor Spirit (PMS) zuwa Naira 1,175 kan kowace lita, bayan da ta janye rangwamen Naira 100 da ta sanar a farkon makon nan. Rahotanni sun ce tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya ne ya ƙara tsadar tace mai.
Wani jami’i a matatar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an ɗaga farashin ne bayan an rage shi zuwa Naira 1,075 kan lita a ranar 10 ga Maris 2026, abin da ya sa ‘yan kasuwar depots suka fara saye da yawa. Sai dai sabon sauyin farashin ya janyo dakatar da ciniki a wasu wuraren ajiyar mai domin jiran karin bayani kan sabon tsarin farashin.
Rahotanni sun nuna cewa tashin farashin na da alaƙa da rikicin siyasa da ya ƙara kamari a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka, Iran da Isra’ila, wanda ya haifar da tashin farashin mai a duniya. Farashin Brent crude ya haura dala 100 kan kowace ganga, yayin da man Najeriya Bonny Light shi ma ya haura wannan mataki sakamakon tashin hankali a kasuwar makamashi ta duniya.
