Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ko wata kujera ba a zaben shekarar 2027. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya ce ba shi da niyyar tsayawa takara.
Saraki ya kuma jaddada cewa jam’iyyar PDP na nan daram duk da rikice-rikicen cikin gida, yana mai cewa karfin jam’iyyar yana nan a matakin kasa da kuma a karkara. Ya ce ra’ayoyin da ke nuna jam’iyyar ta mutu na fitowa ne daga bangaren shugabanni ba daga al’umma ba.
Ya kuma karyata jita-jitar cewa yana shirin komawa wata jam’iyya, yana mai cewa yana nan daram a PDP. Haka kuma ya bayyana cewa ba ya da wata gaba da Shugaba Bola Tinubu kan rikice-rikicen siyasa da suka faru a baya.

