Dakarun rundunar sojin Najeriya ta shiyya ta 6, tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro, sun cafke mutane 28 da ake zargi da satar man fetur tare da lalata gidan tace mai na bogi guda huɗu a cikin ayyukan da suka gudanar daga 6 zuwa 19 ga Oktoba, 2025, a yankin Neja Delta. Sojojin sun kuma kwato sama da lita 290,000 na danyen mai da aka sace a wasu jihohin yankin, musamman a jihar Rivers.

Bayanin hakan ya fito ne daga Lt. Col. Danjuma Jonah Danjuma, mai magana da yawun rundunar, wanda ya ce an gano ƙananan jiragen ruwa (boats) biyu da ke ɗauke da man fetur a Okrika, yayin da ake ƙoƙarin zubawa daga jirgin ruwa zuwa ɗaya daga cikin jety na yankin. Haka kuma, an kama wani jirgin katako ɗauke da lita 33,000 da wani kuma mai ɗauke da lita 5,000 na man sata.

A gefe guda kuma, Kungiyar Ijaw National Congress (INC) ta bayyana cewa jama’ar Ijaw ba za su sake yunƙurin tayar da hankali wajen neman ’yanci ko adalci ba. Shugaban ƙungiyar, Farfaesa Benjamin Okaba, ya ce lokaci ya yi da za a ci gaba da yaƙi ta hanyar ilimi da tunani, ba da bindiga ba, domin neman hakkinsu kan albarkatun yankin.

Ya ƙara da cewa INC za ta ci gaba da magana kan rashin adalci da wariya da ake nuna wa mutanen Ijaw, tare da tsara sabbin hanyoyin neman tabbatar da ikon su kan albarkatun ƙasarsu. Wannan bayani ya fito ne yayin taron kaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar a yankin gabas, wanda ya gudana a Port Harcourt, jihar Rivers.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version