Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya jinjinawa jami’an tsaro bayan nasarar ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin bautar ƙasa 15.
Tinubu ya ce haɗin gwiwar sojoji, ’yansanda, jami’an DSS da kuma masu sa-kai ne suka gudanar da aikin ceton, inda aka kuɓutar da waɗanda aka sace daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ofu.
Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar, yana mai jaddada cewa duk wanda ke da hannu a lamarin, ciki har da waɗanda suka taimaka musu, zai fuskanci hukunci bisa doka.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, domin su samu damar zirga-zirga cikin ƙasar ba tare da fargaba ba.
