Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Daraktan Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).
Naɗin na jiran amincewar Majalisar Dattawa bisa tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta 2006.
Shugaban ya aike da wasiƙa ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, yana neman a gaggauta tabbatar da naɗin.
Ambasada Yusuf zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan kusan watanni 14 a kan muƙamin.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne da ya wakilci Najeriya a matsayin Jakada na musamman a Jamhuriyar Türkiye daga 2021 zuwa 2024.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, a ranar 11 ga Fabrairu, 2026.

