Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya kama hanya tare da mai ɗakinsa zuwa Birtaniya domin amsa gayyatar ziyarar aiki da fadar ƙasar ta yi masa. Bidiyo da gidan talabijin na NTA da fadar shugaban ƙasa suka wallafa ya nuna yadda shugaban da mukarrabansa suka tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport zuwa birnin London.

Wannan ita ce ziyara ta farko cikin shekara 37 da wani shugaban Najeriya ke kai wa fadar sarkin Birtaniya bisa gayyata. Ana sa ran King Charles III da Queen Camilla za su tarbi shugaban yayin ziyarar, inda aka shirya gudanar da manyan liyafa domin girmama shi.

Ziyarar na da muhimmanci wajen ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Birtaniya, tare da tattauna hanyoyin haɗin gwiwa. Rabon da irin wannan ziyara ta faru tun a 1989 lokacin da Ibrahim Babangida ya ziyarci Queen Elizabeth II, yayin da wannan ziyara ke zuwa kwana ɗaya bayan hare-haren Boko Haram da suka yi ajalin mutum 23 a jihar Borno.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version