Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Iran barazanar kai hari idan ba ta amince da wata yarjejeniya ba tare da buɗe mashigar Hormuz cikin wa’adin sa’o’i 48. Ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce lokaci na ƙurewa ga Iran.

Trump ya tunatar da cewa a baya ya bai wa Iran wa’adin kwana 10 domin ta amince da yarjejeniyar ko ta buɗe mashigar, yana mai cewa yanzu saura sa’o’i 48 kacal kafin su fuskanci mummunan hari. Ya bayyana hakan da kalaman gargadi mai tsauri kan abin da ka iya biyo baya.

A ranar 27 ga watan Maris ne shugaban ya sanar da dakatar da duk wani hari kan cibiyoyin makamashin Iran na tsawon kwana 10, matakin da ake ganin wani ɓangare ne na matsin lamba ga ƙasar domin ta amince da buƙatun Amurka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version