Shugaban Kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote, ya yi gargadin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya tilasta Najeriya da wasu ƙasashen Afirka komawa tsarin aiki daga gida kamar yadda aka yi a lokacin COVID-19. Ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Legas.
Dangote ya ce hauhawar farashin mai da rashin tanadi a ƙasashen Afirka na iya jefa jama’a cikin ƙunci, musamman waɗanda ke dogaro da abin da suke samu kullum domin rayuwa. Ya yi nuni da cewa wasu ƙasashe kamar Indonesia sun riga sun rage kwanakin aiki ko kuma suna shirin komawa aiki daga gida idan matsalar ta ƙara tsananta.
Ya kuma bayyana cewa wannan rikici zai fi shafar talakawa da masu ƙananan sana’o’i, musamman waɗanda ke amfani da janareto wajen gudanar da harkokinsu. Dangote ya buƙaci a yi addu’a da kuma haɗin gwiwar ƙasashen duniya domin kawo ƙarshen rikicin, yana mai cewa tasirinsa zai ƙara tsananta tattalin arziki da rayuwar jama’a.

