A cikin sa’o’i 72 da suka gabata, ’yan bindiga sun kai hare-hare a jihohin Kebbi da Adamawa, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu. A Madagali da ke jihar Adamawa, mahaifar gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, rahotanni sun ce an kashe fiye da mutum 24, yayin da hukumomi ke tattara sahihin adadi.
A jihar Kebbi kuwa, maharan sun kai hari masallaci a Dadinkowa, karamar hukumar Maiyama, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata wasu yayin Tafsirin Alƙur’ani da sallar Tarawihi. Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da harin, tana mai cewa ana ci gaba da bincike tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Haka kuma an samu sabbin sace-sace a Sokoto da Kwara, inda aka yi garkuwa da mutane da dama a Rabah da Babanla. A Kwara, matasa sun yi zanga-zanga a Ilorin suna neman a kawo ƙarshen hare-haren, yayin da hafsan sojin ƙasa ya buƙaci a ƙarfafa rundunar sojin sama domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa.

