Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta ɗaukar batun ta’addanci da wasa, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan ta’addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya.

Fagbemi ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin yayin fara wani sabon zagaye na shari’un ta’addanci da suka haɗa da ɗaruruwan mutane. Ya ce wannan shi ne zagaye na huɗu na irin waɗannan shari’u tun bayan hawan gwamnatin yanzu kan mulki.

Ministan ya ce kusan mutum 600 ne za su fuskanci shari’a a wannan zagaye, inda mutum 490 za a gurfanar a ranar Litinin, sannan wasu 84 a rana ta gaba, baya ga wasu 102 da aka ɗauko daga shari’ar da ta gabata. Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da Najeriya ta zama ƙasa mai aminci ga kowa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version